Bashir Usman Tofa Cc s c s4 F
| Bashir Usman Tofa | |
|---|---|
| Rayuwa | |
| ƙasa | Nijeriya |
| Sana'a | |
| Sana'a | ɗan siyasa |
| Imani | |
| Jam'iyar siyasa |
National Republican Convention |
Bashir Usman Tofa ko kuma Bashir Othman Tofa dan siyasa ne a Najeriya. Musulmi kuma Bahaushe wanda ya taso a birnin Kano, Tofa shine dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar National Republican Convention (NRC) a zaben da gwamnatin soja ta Ibrahim Babangida ta shirya a shekarar 1993.
Rayuwar sa[gyara sashe | Gyara masomin]
An haifi tofa a Kano a watan ranar 20, ga Yuni na shekarar 1947. Yayi makarantar firamare ta Shahuci Junior primary school Kano, sai ya cigaba da karatu a makarantar City Senior Primary School a birnin na Kano. Tsakanin 1962-1966 ne , ya halarci makarantar Provinceianl College Kano. Bayan kammala karatu a wannan makarantar ne ya fara aiki da kamfanin Royal Exchange Insurance tsakanin 1967-1968. Daga 1970 zuwa 1973 ya je makarantar City London College Tofa ya shiga harkar siyasa ne a 1977 lokacin da yayi Kamsila a mazabar Dawakin Tofa. Sai aka sake zabarsa mamba a majalisar jaha. A jamhjriya ta biyu ne Tofa ya zama sakataren jam'iyyar NPN a jahar Kano har na wasu lokuta. Sannan kuma ya zama sakataren kudi na jam'iyyar .
A jamhuriya ta uku kuma , Tofa ya hade da jam'iyyar NRC a 1990. A 1993 lokacin Janar Badamasi Babangida yana shugaban soja a Najeriya ne ya shirya tare da gabatar da tsari OPTION A4, aka zabi Tofa a matsayin dan takarar shugaban kasa mai wakiltar kano kuma ya kayar da Pere Ajunwa da Joe Nwodu da Dalhatu Tafida a zaben fidda gwani inda ya dauki tikitin yima jam'iyyar ta NRC takara. Tofa ya yi takara da Sylvesta Ugo a matsayin mataimakin sa.
Tafa yayi rashin nasara a zaben hannun Moshood Kaahimawo Olawole Abiola, bayarbe daga yankin yammacin kasar. Amma daga bisani gwamnatin ta Babangida bata fidda cikakken sakamakon zaben ba.
Tofa kuma dan kasuwa ne , dan kasuwar Mai ne da kuma masana'antu. Shine shugaban kamfanin INTERNATIONAL PETRO-ENERGY COMPANY (IPEC) da kuma ABBA OTHMAN AND SONS LTD. kuma yan zaman mamba a kungiyar Century Merchant Bank and General Metal Products.